An hana mutane yin rashin lafiya a wani gari a Italiya

Asibiti a Italiya
Image caption Wannan asibitin an gina shi ne tun karni na 15

Magajin wani karamin gari a kasar Italiya ya kafa wata doka mai cike da rudani ta hana jama'ar garin kamuwa da rashin lafiya.

Alberto Bambini, magajin garin Acquapendente, ya ce yana son jawo hankali ne kan matakin da gwamnan yankin ya dauka na rufe asibitin garin.

Daga ranar 1 ga watan Janairu, zai zamanto babu wani asibiti a garin sai dai na gaggawa.

Magajin garin ya ce jama'a su guji kamuwa da rashin lafiyar da za ta bukaci a kaisu asibiti, musamman ta gaggawa.

Yana maganar cewa ya yi hakan ne domin "an harzuka shi", ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu ya yi rashin lafiya to "za a hukunta shi ta hanyar kaishi asibitin Belcolle "da ke da nisan mil 30 daga garin.

Ko kuma a ci tararsa kwatankwacin girman cutar ta sa. Mista Bambini ya kuma gargadi jama'a da su kaucewa duk wani abu da zai gurbata musu lafiya, yana mai shawartarsu da su daina barin gidajensu kodayaushe a bude.

Ya shaida wa BBC cewa "yana son bujuro da irin matsalolin da jama'ar yankin ke fuskanta".

Rahotanni sun nuna cewa yankin Lazio na da gibi mafi girma a bangaren lafiya na kasar Italiya.

Duk da cewa ana girmama tsarin lafiyar Italiya a duk duniya, matsalar tattalin arziki ta tilastawa gwamnati rage kudin da take kashewa a fannin.