Mutanen Nijar sun amince da sabon tsarin mulki

Shugaban mulkin sojin Nijar
Image caption Hankali zai koma kan mika mulki ga farar hula

Jama’ar jamhuriyar Nijar sun amince da sabon kudin tsarin mulkin kasar.

Da yamman nan ne aka bayyana sakamakon zaben kuri'ar raba gardamar da aka gudanar a kasar a karshen mako.

An gudanar da kuri’ar ne don nuna amincewa da sabon kudin tsarin mulkin kasar.

Idan an amince da shi ne za a gudanar da zabukan da za su mayar da kasar a kan turbar dimokuradiya.

Mutane kimanin miliyan uku da rabi ne suka kada kuri'ar raba gardamar, kuma kashi tisi’in cikin dari daga cikinsu sun amince da wannan kundi, wanda zai bada damar shirya zabubbuka a farkon shekara mai zuwa.