An gabatar da wasu matasa da ake zargi da fasa bututun mai a Lagos

Matsalar malamar mai a Niger Delta
Image caption Matsalar malalar mai a Niger Delta

A Nigeria, yau ne rundunar sojin ruwa, shiyyar kudu maso yammacin kasar ta gabatar da wasu matasa 18 da ake zargi da yunkurin fasa bututun man fetur dake gabar ruwan tekun Takwabe dake a Lagos.

Kamen na baya-baya, ya zo ne a daidai lokacinda gwamnatin tarayya take lalubo hanyoyin warware matsalolin yankin Naija-Delta da kuma yawaitar fasa bututan matatun man fetur a kasar.

Tuni dai aka mika su ga rundunar tsaro ta 'yan sanda dan gurfanar da su a gaban kotu.

Matsalar fasa bututun mai dai tana janyo wa Nijeriya asara mai yawa inda yawan man da take fitarwa wajen kasar ke raguwa.