Masu sa ido sun yi na'am da zaben Tanzaniya

Tanzania
Image caption Magoya bayan shugaban Tanzaniya Jakaya Kikwete

Masu sa ido na kasa da kasa sun bayyana gamsuwar su da zaben kasa baki dayan da aka gudanar ranar Lahadi a Tanzaniya.

Shugaban tawagar sa'ido ta kungiyar Commonwealth, Paul East, ya shaida wa BBC cewa an samu ci gaba idan aka kwatanta da zaben da aka gudanar shekaru biyar da suka wuce.

Sai dai Mista East ya ce abin takaici ne ganin yadda aka dauki tsawon lokaci ba a bayyana sakamakon zaben ba.

Ya kara da cewa ganin yadda ake da kayan aiki na zamani, bai kamata sakamakon ya haura kwanaki hudu zuwa biyar ba.

Tun da farko jam'iyyun hamayya sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da yadda ake jan kafa wajen bayyana sakamakon zaben.