Burtaniya da Faransa sun kulla yarjeniyoyin tsaro

Burtaniya da Faransa
Image caption Labour ta ce akwai alamun tambaya kan makomar tsaron Burtaniya

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ta Pira Ministan Burtaniya David Cameron, sun rattaba hannu kan wasu sabbin yarjeniyoyin tsaro biyu.

Kasashen wadanda dukkaninsu mambobin kungiyar tsaro ta NETO ne sun ce, yarjejeniyar ta bude wani sabon shafi na hadin kan soji ba tare da yin zagon kasa ga 'yancin kasa ba.

Pira Minista David Cameron yace: "sakamakon yarjejeniyar zai kare lafiya da samar da tsaro ga 'yan kasar mu a wannan lokaci da muke ciki na rashin tabbas.

A cikin yarjejeniyar za'a horas da rundunar ko ta kwana ta Faransa da Burtaniya, da ma girke wani jirgin ruwan daukar jiragen sama a gabar ruwa wanda zai kasance a wajen ko da yaushe.

Sa'insar siyasa

Fadar mulkin Burtaniya ta Downing Street ta bayyana shirin da cewa "na zahiri ne", yayinda jam'iyyar adawa ta Labour ta ce akwai alamun tambaya kan makomar tsaron Burtaniya.

Mai magana da yawun Downing Street ya ce: "Wannan taron wani babban mataki ne na dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Abinda muke yi shi ne hada kai domin fuskantar manyan matsalolin da ke gaban mu."

Wannan taron dai na zuwa ne makwanni biyu bayan da gwamnatin Burtaniya ta bada sanarwar rage kudaden da take kashewa kan sojojin kasar, a wani kokari na rage gibin da kasar ke fama da shi.

Shirin zai kuma kai ga kafa wata cibiyar bincike a Burtaniya da kuma wata a Faransa domin yin gwajin.