Bush ya koka kan kasa gano makamai a Iraqi

Tsohon shugaban kasar George W Bush
Image caption Bush ne ya jagaoranci mamayar da Amurka ta yiwa Iraqi

Kafofin yada labaran Amurka sun ambato tsohon shugaban kasar George W Bush, yana cewa har yanzu yana takaicin rashin ganin makaman kare-dangi a Iraqi.

Bayanan sun bayyana ne a wani littafi da ya rubuta kan matakan da ya dauka lokacin yana kan karagar mulki "Decision Points", wanda za a wallafa mako mai zuwa.

Ya kuma bayyana cewa akwai lokacin da ya yi tunanin cire mataimakinsa Dick Cheney.

Sai dai bai ce komai game da mutumin da ya gaje shi ba wato Barack Obama.

Tsohon shugaban mai shekaru 64, ya kare matakin da ya dauka na mamaye kasar Iraqi a tarihin rayuwarsa da ya rubuta, wanda jaridar New York Times ta samu.

'Cire Dick Cheney'

Ya bayyana cewa Iraqi za ta fi zamowa kasa mafi kyau ba tare da Saddam Hussein ba, wanda ya bayyana a matsayin "dan kama-karya".

Sannan yace Amurka ma sai ta fi zama lafiya yayinda aka kawar da Saddam, wanda ke kokarin mallakar makaman kare-dangi. Sai dai yace ya girgiza kuma ya ji haushi lokacin da aka kasa gano makaman nukiliya a kasar ta Iraqi.

Shugaban ya ce ya shafe makwanni yana tunanin sauya Mista Cheney da Sanata Bill Frist a lokacin zaben shekara ta 2004.

Tunanin ya zo ne a wata ganawa da Bush ya yi da mista Cheney a shekara ta 2003, wanda ya nemi ya ajiye mukamin don radin kansa.

"Na yi tunanin amincewa da bukatar ta sa," a cewar Mista Bush, kamar yadda jaridar New York Times ta bayyana.