Girka ta dakatar da aika sakwanni waje

'Yan sandan kasar Girka
Image caption 'Yan sandan kasar Girka

Hukumomin kasar Girka sun dakatar da tura sakwanni ta jiragen sama zuwa kasashen ketare har tsawon sa'o'i arba'in da takwas.

Dakatarwar ta biyo bayan aikewa da wasika mai dauke da bom ne zuwa ga Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, da kuma fashewar wadansu bama-baman da ke kunshe a cikin sakwanni a ofisoshin jakadancin Rasha da Switzerland da ke Athens babban birnin kasar.

Firayim Ministan Girka, George Papendreou, ya ce gwamnatinsa za ta yi bakin kokarinta domin tabbatar da tsaron yan kasar.

“Mu a wajenmu tsaron ’yan kasa hakki ne a kan gwamnati, wato tsaron rayukansu, da ayyukansu, a kowanne hali su ke ciki a kowanne lokaci”, inji shi.

Jami'an tsaro dai na zargin wata kungiyar Girkawa masu ra'ayin gurguzu ne ke aikewa da wadannan sakwannin na ta'addanci.