Mai yiwuwa Gbagbo da Ouattara su fafata

Shugaba Laurent Gbagbo
Image caption Shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast

Sakamakon da aka samu ya zuwa yanzu na zaben shugaban kasar Ivory Coast ya nuna cewa mai yiwuwa sai an yi zagaye na biyu a karshen watan Nuwamba kafin samun wanda ya yi nasara.

Bayan kidaya rabin kuri'un da aka kada dai, sakamakon ya nuna cewa Shugaba Laurent Gbagbo da kuma tsohon Firayim Minista Alassane Ouattara sun yi kankankan da kashi talatin da biyar cikin dari na kuri'un ko wannensu.

A zabuka biyun da suka gabata dai an haramtawa Ouattara tsayawa takara, al'amarin da ya haddasa rikice-rikice a kasar.

Shi kuwa dan takara na uku, Henri Konan Bedie, na biyewa wadannan 'yan takara biyu ne da kashi ashirin da bakwai na kuri'un da aka kirga ya zuwa yanzu.

Idan sakamakon bai sauya ba kuma, magoya bayansa za su taka muhimmiyar rawa a zagaye na biyu na zaben.

Shi dai Bedie kusa ne a kawancen jam'iyyun adawa tare da Ouattara; to amma masu nazari na nuna shakku a kan ko magoya bayansa za su bi umurni su zabi Ouattaran.

Idan dai ba an samu wani sauyi ba, wadannan kuri'u na Bedie ne za su yanke hukunci a kan wanda zai yi nasara tsakanin Gbagbo da Ouattara.