Wata tankar mai ta yi hadari a jihar Kano

Taswirar Nijeriya

Wata motar daukan man fetur shake da man, wadda ta taso daga Kano zuwa jihar Bauchi ta fadi a kusa da gidajen jama'a a garin sabuwar kasuwa, cikin karamar hukumar Albasu dake jihar Kano.

Babu dai wanda ya rasa ransa, amma hadarin ya janyo asarar dukiyoyi inda gidan da motar ta fada kansa ya kone kurmus.

Rashin kyawun hanyoyi da gangancin direbobi dai na daga matsalolin da ke jawo dimbin hadururrukan ababan hawa a Najeriya, abinda ke jawo asarar dubban rayuka da dukiya a kasar.