'Yan adawa a Najeriya sun soki Dalhatu Tafida

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A Najeriya wadansu 'yan adawa sun soki jagoran yakin neman zaben Shugaba Goodluck Jonathan, Dokta Dalhatu Sarki Tafida, bisa tauna taura biyu—jan ragamar yakin neman zaben shugaban kasar da kuma aikinsa na jakadan Nigeria a Burtaniya.

’Yan adawar sun kuma yi kira a gare shi da sauran manyan jami'an gwamnati da suka yi dumu-dumu a harkar siyasa su zabi daya.

Masu wannan zargin sun kuma yi korafin cewa bai kamata ace ana biyan Dokta Dalhatu Sarki Tafida albashin jakada a Buraniya ba tunda ya jima da barin ofishinsa da ke London.

Daya daga cikin ‘yan adawar da ke da wannan ra’ayi, Injiniya Buba Galadima na jam’iyyar CPC, ya ce ya kamata a ce Dokta Tafida “ko ba a gaya ma[sa] ba, [ya] san ba daidai ba; [don haka sai ya zabi daya: ko ya yi aikin Goodluck, ko kuma ya koma kan akinsa na jama’ar Najeriya ya wakilce su”.

Shi dai Dokta Dalhatu Sarki Tafida yana Najeriya a yanzu inda yake yawon tallata Shugaba Goodluck Jonathan a zabe mai zuwa.

Sai dai kungiyar yakin neman zaben shugaban kasar ta yi watsi da wannan suka inda ta ce masu korafin basu da abin yi ne.

Kakakin kungiyar, Sully Abu ya shiadawa BBC cewa abin da Dokta Tafida ya yi yana bisa ka’ida saboda “ya dauki hutun wata uku, kuma akwai jakadan wucin gadi—mataimakinsa—kuma tun kafin ya zama jakada shi dan siyasa ne ba jami’in diflomasiya ba”.