'Yan Republican za su ja da Obama

John Boehner
Image caption Jagoran 'yan jam'iyyar Republican a Majalisar Wakilai, John Boehner

Jagoran Republican a Majalisar Wakilan Amurka John Boehner, ya nemi shugaba Obama da ya sauya wasu manufofinsa, bayan da jam'iyyarsa ta sha kayi a zaben rabin-wa'adin da aka gudanar.

Alkaluman sakamakon zaben rabin-wa'adi a Amurka sun nuna cewa jam'iyyar adawa ta Republican ta karbe jagorancin Majalisar Wakilai ta kasar.

Jam'iyyar Democrat ta Shugaba Obama ta rasa rinjayen da ta ke da shi a Majlisar ne bayan masu kada kuri'a sun tashi 'yan jam'iyyar da dama daga kujerunsu.

'Yan jam'iyyar ta Republican, da kuma abokan tafiyarsu na gamayyar masu ra'ayin mazan jiya ta Tea Party, sun yi nasarar karbe fiye da kujeru talatin da taran da suke bukata don yin rinjaye a Majalisar.

Yayin da ya ke jawabi ga magoya bayan jam’iyyar ta Republican, shugaban marasa rinjaye a Majalisar, wanda kuma yanzu ya ke da tabbacin darewa kujerar shugaban masu rinjaye, John Boehner, ya ce wannan nasara da jam'iyyarsa ta samu gargadi ne ga Shugaba Obama daga al'ummar kasar.

“Ko da yake rinjayen mu zai ba ku karfin fada a ji a Majalisa, wajibi ne mu tuna cewa shugaban kasa ne ya ke tsara alkiblar gwamnati.

“Wannan nasara [tamu] kuma sako ne karara da mutanen Amurka suka aike masa cewa ya sauya alkibla”.

Sai dai alamu sun nuna cewa duk da cewa jam'iyyar ta Democrat ta yi asarar kujerun Majalisar Dattijai a wasu jihohi, nasarar da ta yi a wasu jihohin ta sa ba za ta rasa rinjayenta a Majalisar Dattijan ba.

Image caption Shugaba Obama yana magana da jagoran Republicans

Wannan kuma na da matukar muhimmanci ga Shugaba Obama don aiwatar da wadansu manufofi na gwamnatinsa.

Rahotanni dai sun bayyana cewa daga cikin kujerun Majalisar Dattijan da jam'iyyar Democrat ta rasa har da wadda Shugaba Obama ya ke kai kafin ya zamo shugaban kasa.

Fadar White House ta ce Shugaba Obama ya kira Mista Boehner ta wayar tarho, inda ya bukaci su yi aiki tare don cimma manufa guda bayan zaben rabin-wa'adin.

Kujerun Majalisar Dattijai shida jam'iyyar Republicans ta kwace daga hannun Democrats.

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da gidan talabijin an ABC ya gudanar ta nuna cewa kashi 88 cikin dari na Amerikawa sun yi imani da cewa tattalin arzikin kasar na cikin matsala - kusan daidai da adadin da suka bayyana haka gab da zaben Obama.

Kamar yadda binciken ya nuna, kashi 73 cikin dari sun bayyana rashin amincewa da yadda gwamnatin tarayya ke tafiyar da al'amura, yayinda kashi 26 daga cikinsu suka ce su ransu ma a bace yake.

"Wannan ba karamin koma baya bane ga shugaban da aka zaba da gagaramin fata da kuma kwarin guiwa," Mark Mardell Editan BBC a Arewacin Amurka.

Baya ga zabukan 'yan majalisu, wasu jahohin sun zabi gwamnoni

* John Kasich ya doke Ted Strickland a Ohio, abinda ya baiwa Republicans iko da jihar da za ta yi tasiri a zaben shugaban kasa na 2012.

* A California, dan Democrat Jerry Brown ya doke Meg Whitman na Republican, tsohon shugaban kamfanin eBay.

* A New York, Andrew Cuomo na Democrat ya lashe ofis din da mahaifinsa ya rike a shekarun 1980 da karshen 1990.

A wasu jihohin dai jam'iyyar da ke da rinjaye a majalisun jihohi kuma take da kujerar gwamna, tana da fada aji kan yadda za a sake tsara alkiblar mazabun gundumomi a shekaru 10 masu zuwa.

Karin bayani