BBC ta nemi afuwa a bisa kuskuren da ta yi

Bob Geldof
Image caption Jagoran kungiyar agaji ta Band Aid, Bob Geldof

BBC ta nemi afuwa bayan ta yi ikirarin cewa an karkatar da miliyoyin kudaden da wata kungiyar bayar da tallafi mai suna Band Aid ta tarawa kasar Habasha don yakar yunwa zuwa ga sayo makamai.

A watan Maris ne wani shirin BBC mai suna Assignment ya gudanar da bincike don gano ko kudaden agaji a shekarun 1980 sun zarce aljihun 'yan tawaye a kasar ta Habasha.

Shirin dai bai fito karara ya ce an karkatar da kudaden na Band Aid ba, to amma hukumar BBC ta yarda cewa mai yiwuwa shirin ya yi nuni da hakan.

Sai dai wasu kafofin labarai na BBC sun bayyana cewa 'yan tawaye sun karkatar da miliyoyin kudaden na BandAid.

Jagoran kungiyar, Bob Geldof, ya fusata, yana mai cewa BBC ba ta hujjar da za ta tabbatar da wannan ikirari, sannan hukumar gudanarwar kungiyar ma ta yi korafi.

Da fari dai BBC ta kare labarin, amma bayan sashenta na sauraron korafe-korafe ya gudanar da bincike, ta nemi afuwa daga kungiyar ta BandAid da kuma Bob Geldof, tana mai cewa wadansu daga cikin rahotannin sun yi nunin da ya kauce ka'ida.

Bob Geldof ya yi na'am da neman afuwar, yana mai cewa rahotannin kuskure ne da a saba ganin irinsa ba.