Najeriya ta kori 'yan kasashen waje da dama

Jami’an shige da fice na Nigeria sun ce, sun fitar da bakin haure dari bakwai daga arewacin kasar.

Hukumar shige da ficen ta ce ta dauki wannan matakin ne da nufin inganta matakan tsaro kafin zuwan babban zaben kasar da za a yi a badi.

Shugaban hukumar, Babayo Alkali, ya ce bakin hauren daga kasashen Cameroon da Chad da Nijar, sun samu shiga kasar ne ta haramtacciyar hanya domin kada kuria a zabukan kasar.

A bangare guda kuma majalisar dokokin kasar ta amince da dokar dage lokacin zaben daga watan Janairu zuwa watan Afrilu, domin bada damar shirya zaben a tsanake.