Shugaba Obama zai tattauna sabuwar alkiblar kasar

Shugaba Obama
Image caption Ko 'yan Republican za su ba Obama hadin kai?

Shugaba Barack Obama na Amurka ya gayyaci shugabannin jamiyyun Republican da na Democrats a majalisar dokokin kasar zuwa fadar gwamnatin kasar ta White House.

Ya kira wannan ganawa ne bayan kayen da jamiyyarsa ta Democrats ta sha a zaben rabin wa’adi, inda ta rasa rinjayen da take da shi a majalisar wakilai.

Bayan kammala taron majalisar zartarwa, Shugaba Obama ya shaida wa manema labaru cewa:

“A bayyane take cewa abinda ke da matukar muhimmanci cikin watannin dake tafe shi ne mu inganta dangantakar aiki tsakanin fadar White House da shugabannin majalisar dokokin da suka shigo, da kuma wadanda suka karbi jagoranci daga majalisar da ta gabata.”