An tuhumi wasu Amerikawa da tallafawa Al Shabab

Somalia
Image caption Al Shabab na fada ne da gwamnatin Somalia, wacce kasashen duniya ke marawa baya

A karo na biyu cikin 'yan kawanaki masu gabatar da kara a Amurka, sun tuhumi wasu Amerikawa da tallafawa kungiyar masu fafutukar Islama ta Al Shabab da ke Somalia.

An zargi wani matukin motar tasi (Mohamud Abdi Yusuf) daga St Louis, da wani ma'aikacin kamfanin hada-hadar kudade a garin Minneapolis (Abdi Mahdi Hussein), da tallafawa kungiyar da dubban daloli.

Harwa yau an zargi mutum na uku Duane Mohamed Diriye, shi ma da laifin tallafawa kungiyar ta Al Shabab. Ana kyautata zaton yana Somalia ko Kenya.

An gabatar da makamantan wadannan zarge-zarge kan wasu 'yan Somalia uku ranar Talata da ke zaune a birnin California.