Kasashe matalauta suna samun cigaba da sauri

Yankin marasa galihu
Image caption Talakawa za su gani a kasa

Shirin Samar da Cigaba na MDD, UNDP, ya ce wasu daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya su ne suke samun ci gaba cikin sauri ta fannin inganta rayuwar alummominsu.

Shirin ya ce kididdigar shekara-shekara na ci gaban rayuwar mutane, ta nuna cewa aikin ceto ya samu nasara sosai ta fuskar lafiya da samar da ilmi, wadanda su ne kashin bayan aikin shirin.

Shugabar UNDP din Helen Clark, ta bayyana cewa, “Babbar gudumuwar da aka samu wurin hada wannan rahoto ita ce, yadda aka yi nazari kan ci gaban rayuwar mutane cikin tsari, inda aka gudanar da bincike a kasashe 135 daga shekaru 40 zuwa yanzu.

Wannan kididdiga ta nuna cewa rayuwar mutane a yau ta fi koshin lafiya da yalwar ilmi fiye da a baya