Bankin Amurka zai gurza sabbin kudade

Ben Bernanke
Image caption Shugaban Babban Bankin Amurka, Ben Bernanke

Babban Bankin Amurka ya bayar da sanarwar wani sabon shiri na farfado da tattalin arzikin kasar ta hanyar sakin dala biliyan dari shida don tallafawa tattalin arzikin.

Bankin na Amurka ya ce zai karbi bashi ne daga kasuwannin hadahadar hannayen jari, ya kuma biya ta hanyar gurza sababbin kudade.

Hakan zai rage yawan kudin ruwan da gwamnati ke biya a kan basussukan da ake bin ta ya kuma karawa magidanta da 'yan kasuwa kwarin gwiwar kashe kudi.

Haka nan kuma matakin na Babban Bankin zai kara darajar hannayen jari, al'amarin da zai karawa al'ummar kasar wadata, ya kuma sa su kara fitar da kudi.

Manufar wannan mataki dai ita ce zaburar da tattalin arzikin kasar wanda ya ke saibi da yawa wajen farfadowa.

Kashi tara da digo shida cikin dari na ma'aikatan kasar ne dai ba su da aikin yi, yayin da wadansu da dama kuma, wadanda ba a shigar da su cikin wannan lissafi ba, ke da sha'awar yin aikin, amma babu.

Hadarin da ke tattare da wannan mataki dai shi ne zai iya sa farashin kayayyaki ya yi tashin gwauro zabi.

Wannan dalili ne ya sa daya daga cikin mambobin kwamitin gudanarwar Bankin ya kada kuri'ar kin amincewa da matakin, yana mai gargadin cewa zai iya sukurkuta tattalin arzikin.