Jirgi ya fadi a Cuba, ya kashe mutane 68

Jirgin saman kasar Cuba da ya yi hadari
Image caption Jirgin saman kasar Cuba da ya yi hadari

Wani jirgin saman kamfanin Aero Caribbean, mallakar gwamnatin kasar Cuba, ya fadi a tsakiyar kasar.

Jirgin saman ya fadi ne a kusa da kauyen Guasimal da ke lardin Sancti Spiritus.

Gidan talabijin na gwamnatin kasar ya bayar da rahoton cewa akwai fasinjoji sittin da daya da ma'aikata bakwai a cikin jirgin.

Babu wani daga cikin mutanen da ke cikin jirgin da ya tsira da ransa.

Ashirin da takwas daga cikin fasinjojin dai 'yan kasashen waje ne.

Ko da yake ba a bayar da sunayen fasinjojin ba, kafofin yada labarai na gwamnatin kasar sun bayyana kasashen da mutanen suka fito.

Akasarinsu dai sun fito ne daga nahiyar Latin Amurka, goma kuma mutanen nahiyar Turai ne, sai kuma dan Japan guda daya.

Hukumomi sun bayyana cewa sai da ma'aikatan agaji suka sha wahala kafin su bude hanyar da za ta kai su wurin da jirgin ya fadi ta cikin sunkurun daji.

Jirgin dai, wanda ya kan yada zango a garin Santiago da Cuba, ya kan tashi ne sau biyu duk mako daga birnin Port-au-Prince na kasar Haiti zuwa Birnin Havana na kasar ta Cuba.