Mahaukaciyar guguwa ta dumfari kasar Haiti

Wasu daga cikin matan da aka tasa daga sansanin wucin gadi
Image caption Wasu daga cikin matan da aka tasa daga sansanin wucin gadi

Hukumomi a kasar Haiti sun shawarci dubban mutane su bar sansanonin da suke yayinda ake fargabar wata mahaukaciyar guguwa mai tafiya da ruwa za ta isa kasar a yau.

Sai dai mutanen sun ki tashi daga sansanonin saboda, a cewarsu, ko sun bar wurin ba su da inda za su je.

Tuni dai an fara ruwan sama kamar da bakin kwarya a kasar, yayinda kungiyoyin ba da agaji ke cewa ba zai yiwu a kwashe dukkan mutanen zuwa matsera kafin isar iskar ba.

Masu hasashe sun yi gargadin cewa mahaukaciyar guguwar, wadda suka kira Tropical Storm Tomas, ka iya yin kaca kaca da tantunan da mutanen ke zaune tun bayan da girgizar kasa ta rusa musu gidajensu a watan Janairu.

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a kasar ta Haiti, Nigel Fisher, ya bayyana cewa akasarin mutanen da ke zaune a sansanonin na wucin gadi suna babban birnin kasar ne, Port-au-Prince, inda mahaukaciyar guguwar ba za ta yi karfi sosai ba, amma duk da haka za ta yi ta'adi mai yawa.

Jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma ce ma'aikatan agaji na fatan fiye da kashi hamsin na mutanen za su fake a wurare masu aminci kamar majami'u, duk da cewa lokaci ya riga ya kure.

Ma'aikatan agaji sun ce sun yi shirin kai agajin gaggawa da zarar guguwar ta wuce.

Tuni dai mahaukaciyar guguwar ta hallaka mutane akalla goma sha biyu a tsibirin Saint Lucia a kan hanyarta ta zuwa kasar ta Haiti.