Tsaunin Merapi ya sake tumbudi

Tsaunin Merapi ya sake tumbudi
Image caption Tsaunin Merapi ya sake tumbudi

A kalla mutane 64 ne suka mutu a Indonesia, bayanda tsaunin Merapi ya sake aman wuta, adadin ya ninka wadanda dutsen ya kashe a baya tun sanda ya fara aman a makon da ya wuce.

Daruruwan mutane aka kai asibiti domin duba lafiyarsu, bayan barkewar aman, wanda shi en mafi muni da dutsen ya yi.

A yanzu ana hasashen wadanda suka mutu sun haura dari.

Yayinda aka debe mutane dubu 75 daga gidajensu.

Wani jami'in agaji ya shaidawa BBC cewa ba a zaci karfin aman wutar zai kai haka ba, amma dai da mutanen kauyukan sun amince da zama a sansanin da aka tanada da ba a yi asarar rayuka ba.

Sai dai tattara mutanen a sansanoni ya gagara saboda cunkoso, sannan kuma mutanen ba sa kaunar barin gonakinsu.