An kori ministan ma'adanai na Nijar

Salou Djbou
Image caption Nijar na fuskanci sauye-sauye a 'yan kwanakin nan

A Jamhuriyar Nijar shugaban mulkin sojan kasar, Janar Salou Djibo, ya sauke ministan ma'adinai da makamashi Malam Souleymane Mamadou Abba daga kan mukaminsa.

Shugaban ya kuma ya maye gurbin ministan da Madame Djibo Salamatou Gourouza Magaji.

Ita dai madam Djibo Salamatou dama minista ce a gwamnatin mulkin sojin kasar.

Malam Sabo Gado Mahamane Sani shi kuma aka nada shi ministan raya birane da gidaje inda ya maye gurbin ita Madame Djibo Salamatou Gourouzza Magaji.

Jami'an mulkin sojin sun bada sanarwar ne ba tare da wani karin bayani kan dalilan da suka sa su daukar matakin ba.

A 'yan kwanakin nan dai ana fuskantaer sauye-sauye a gwamantin sojin ta Nijar, a daidai lokacin da zaben kasa baki daya ke kara karatowa.