Harin bom ya kashe mutane 50 a Pakistan

Harin bom ya kashe mutane 50 a Pakistan
Image caption Pakistan ta sha fama da hare-haren kunar bakin wake

A kalla mutane 50 ne aka kashe yayinda fiye da 70 suka jikkata bayan wani dan kunar bakin waye ya tada bom a wani masallaci a Arewacin Pakistan.

An kai harin ne lokacin sallar Juma'a a unguwar Darra Adam Khel, kusa da yankin kasar da ya fi fama da rikici.

Rufin ginin masallacin na mabiya tafarkin Sunni ya rufta, kuma mahukunta sun ce ana saran adadin wadanda suka rasu zai karu.

"Muna tsoron za a samu karuwar wadanda abin ya ritsa da su," a cewar wani jami'i.

Wasu da suka ga abinda ya faru, sun shaida wa BBC cewa maharin ya zo ne a kasa, sannan ya tashi bom din da ke jikinsa a bakin kofa jim kadan bayan kammala sallar Juma'a, lokacin da mutane ke barin masallaci.

Mai yiwuwa an hari wani shugaban al'umma ne wanda ya yi kira ga jama'a su juyawa Taliban baya. Babu tabbas ko yana cikin wadanda harin ya ritsa da su.

Masallacin na kauyen Akhurwal ne, kimanin kilomita 45 a kudancin Peshawar.