Guguwa ta hallaka mutane shida a Haiti

Ambaliyar da guguwar 'Tomas' ta haddasa
Image caption Ambaliyar da guguwar 'Tomas' ta haddasa

Akalla mutane shida ne suka rasa rayukansu bayan da mahaukaciyar guguwan nan mai tafe da ruwa, wato ‘Tomas’ ta keta ta wasu yankunan kasar Haiti.

Sai dai tantunan daruruwan mutanen da suka rasa muhallinsu a girgizar kasar watan Janairu a Port-au-Prince sun jurewa karfin guguwar da ruwan sakamakon matakan da aka dauka tun farko wadanda suka hada da gina magudanan ruwa.

Jami'ai sun ce ruwan ya shanye garin Leogane da ke kudancin kasar, yayinda ya kai iya kwauri a wasu daga cikin sansanonin wucin gadin na Port-au-Prince.

Ta'adin da guguwar ta yi dai ya fi kamari ne a yammacin kasar, yankin da ambaliyar ruwa ta hana kaiwa gareshi daga sauran sassan kasar.

Gwamnati ta ce ta dauki matakan tsugunar da mutanen da abin ya shafa har dubu dari a makarantu da asibitoci, da majami'u.

Tuni dai kungiyoyin bayar da agaji suka ruga don hana yaduwar cututtuka yayinda guguwar ta nausa zuwa yankin da ke fama da annobar cutar kwalara.

Da ya ke jawabi ga al'ummar kasar, Shugaba Rene Preval ya ce kasar na fama da bala'o'i guda biyu, wato mahaukciyar guguwar da kuma cutar kwalara.

Jami’ai dai sun ce za a dauki kwanaki kafin a tantance hakikanin barnar da guguwar ta haifar.