Matsalar ilimin 'ya 'ya mata a Najeriya

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, a wani yunkuri na magance matsalar ilimin yara mata a Arewacin kasar, wata kungiyar mata Musulmi, ta shirya wani taro a Kaduna domin lalubo yadda za'a tunkari wannan matsala.

Matsalar karancin 'ya 'ya mata da ke zuwa makaranta a Arewacin kasar dai na cigaba da jan hankalin masana, da malamai da kuma sauran jama'a.

Wannan lamari ya janyo damuwa ainun, musamman ma irin kyamar da har yanzu jama'ar Arewacin kasar ke nuna wa ilimin boko tun daga na Firamare ya zuwa manyan makarantu.

Bayanai dai na nuni da cewa duk da wayewar kan da aka samu, har yanzu akwai iyayen da ke cigaba da nuna kyama ga ilimin 'ya 'ya mata, musamman ma gudun kada yaran su koyi dabi'u irin na turawa.

A kan haka ne dai kungiyoyin mata ke son wayar da kan iyaye cewa ilimin 'ya 'ya mata na da mahimmanci, domin a addinin Musulunci wajibi ne.