Shugaba Barack Obama na ziyara a Indiya

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Barack Obama na Amurka zai sauka a cibiyar kasuwancin kasar Indiya, Mumbai, don fara wata ziyarar kwanaki goma a nahiyar Asiya.

Tuni dai dubban jami'an tsaro, cikin har da jami'an tsaro na kasar Amurka da kuma zaratan jami'an tsaron kasar Indiya, suka ja daga a fadin birnin na Mumbai.

Haka zalika wani jirgin ruwan yaki na Amurka tare da wasu jiragen na Indiya na ta sintiri a teku.

A yini na farko na ziyarar tasa, Shugaba Obama zai yi bukin tunawa da wadanda harin da aka kai birnin na Mumbai a shekarar 2008 ya shafa, ciki har da Amurkawa da dama wadanda suka tsira da rayukansu.

Sannan kuma Mista Obama, wanda ke samun rakiyar shugabannin wasu manya-manyan kamfanonin Amurka, zai gana da manyan 'yan kasuwar kasar ta Indiya.

Shugaban na Amurka dai ya bayyana fatan cewa Amurka za ta samu karin damar shigar da kayayyakinta kasuwannin kasar Indiya, a wani yunkuri na rubanya yawan kayayyakin da ta ke fitarwa zuwa kasashen waje a shekaru goma masu zuwa da kuma taimakawa wajen farfado da tattalin arzikinta.