Obama ya ce sun zo daya da India a yakar ta'addanci

Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Barrack Obama ya ce, Amurka da India kasashe ne da tasu ta zo daya wajen nuna kyama ga ayyukan ta'addanci.

Shugaba Obama ya yi wannan jawabin a wata ziyara da ya kai birnin Mumbai na kasar India.

Shugaban ya jaddada wannan furucin ne a yayin wani jawabi da ya yi a Otel din Taj Mahal, wanda yana daya daga cikin wuraren da masu tsaurin ra'ayin Islama suka kaiwa hari a shekara ta 2008.

Sai dai kuma Shugaba Obama ya fito fili ya bayyana cewa, shi fa ya kai wannan ziyara ne domin nemarwa kamfanonin Amurka kasuwa a India, wannan a cewarsa, domin ya samarwa da 'yan Amurka ayyukan yi wanda ka iya taimakawa wajen rage kalubalen da yake fuskanta yanzu haka.

Shugaba Obama ya bayyana kulla alakar kasuwanci ta dala biliyan goma tsakanin Amurkar da India.

Tawagar shugaba Obama wadda ta kunshi wasu hamshakan 'yan kasuwar Amurka, ta gana da manyan takwarorin ta na India a birnin Mumbai.