Gawawwakin 'yan bude-ido a Mexico

Taswirar kasar mexico
Image caption An gano gawawwaki a Mexico

An tabbatar da cewa tarin gawawwakin da a ka gano a kasar Mexico na 'yan yawon bude ido ne su goma sha takwas da aka sace.

Mutanen sun bace ne fiye da wata guda bayan da suka bar garuruwansu inda wasu shaidu suka ce, karon karshe da aka gansu,shi ne lokacin da suke neman otal din da zasu kwana a birnin Acapulco.

David Sotelo, shi ne babban mai shari'a a jihar Guerrero wacce ta kunshi garin na Acapulco, ya tabbatar da cewa gwajin da suka yi ya nuna cewa an kashe mutanen ne jim kadan bayan da aka sanar da bacewarsu.

Ya ce:''Sakamakon gwajin da muka yi mun gano cewa tabbas an kashe mutanen ne makwanni hudu da suka gabata''.