Fiye da mutane 500 sun mutu a Haiti

Wani mutum da ke fama da cutar amai da gudawa
Image caption Cholera ta kashe mutane dari biyar a Haiti

Gwamnatin kasar Haiti ta ce fiye da mutane dari biyar ne suka mutu sakamakon annobar cholera da ta bulla a kasar.

Shugaban kasar Rene Preval, ya yi gargadin cewa akwai yiwuwar karuwar annobar sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi tayi.

Ya ce:''Ambaliyar ruwan ta wuce inda yanzu muke duba irin barnar da ta yi, sai dai annobar ta cholera na ci gaba musamman saboda yadda lamari ya kara muni sakamakon kwaso cututtuka da ruwa ke ci gaba da yi''.

Kungiyoyin bada agaji dai na ci gaba da kokarin kai tsabtataccen ruwan sha a yankunan da ambaliyar tafi muni.

Kungiyar bada agaji ta Save The Children ta ce a hanyoyi a garin Leogane, sun koma tamkar koguna inda ambaliyar ruwan ta shafi kimanin mutane dubu talatin .