Yunkurin sasanta musulmai da kiristoci

Taswirar Najeriya
Image caption Malamai sun yabawa yunkurin sasanta musulmai da kiristoci

A Najeriya, malaman addinin musulunci da kiristanci sun yi marhabin da shawarar da wani taro ya yanke ta aikewa da tawagogi kasashen da ke fama da rikice-rikicen addini, domin fadakar da su muhimmancin zama lafiya.

Manyan shuwagabannin addinan ne suka cimma wata yarjejeniya a taron, wanda aka gudanar a Geneva domin su tunkari tashe-tashen hankula da ake dangantawa da addini.

Shuwagabannin addinan dai sun hadu ne karkashin inuwa guda, kuma kungiyoyin da ke kan gaba wajen wannan fafutika, su ne majalisar majami'u ta duniya wato WCC, mai majami'u kimanin 349 da kuma kungiyar da'awar Islama ta duniya wato WICSN mai kungiyayoyi 600 a karkashinta.

Reverend Olav Fykse Tveit, shi ne babban sakataren majalisar majami'u ta duniya.

Ya ce:''Mun gano cewa akwai batutuwa da dama a sassa daban daban na duniya, kamar Asia, da Gabas ta tsakiya da turai da kuma Afirka wadanda daukar wannan mataki wajen tunkaransu, zai dace''.

'Mun yaba da taro'

A nasu bangaren malaman addinin musulinci da na kirista a Najeriya sun ce duk wani yunkuri na fadakar da mabiya addinan muhimmancin zama lafiya abin farin ciki ne.

Sheikh Balarabe Dawud, shi ne babban limamin masallacin juma'a na birnin Jos.

Ya ce:''Idan wata kungiya ta ce za ta yi namijin kokari domin a kawo fahimtar juna da sulhuntawa yadda ba za a rika samun tashin-hankali irin yadda ake samu a kasashe da yawa, har da kasata Najeriya, to wannan babu shakka abin yabo ne.Sai muce Allah ya yi musu taimako''.

Limanin ya ce ana samun tashe-tashen hankula da suka danganci addini a kasar ne sakamakon kyashi, da hassada da wasu ke yi idan Allah ya azurta wasu.

A nasa jawabin, reverend Joseph John Hayap, sakataren kungiyar kiristotci ta Nijeriya, CAN reshen jihar Kaduna, ya bayyana gamsuwarsa da yunkurin sasanta mabiya addinan biyu.

Ya ce suna fadakar da mabiyan su kan muhimmancin zaman lafiya.

Ya kara da cewa:''Muna fadakarwa ga jama'a.Ko dazu(jiya) mun yi wani babban taro inda matasa fiye da dubu biyar suka halarta.Na fadakar dasu kan su guji jita-jita.Kada su yadda 'yan siyasa su yi amfani dasu wajen cimma bukatarsu''