Ana gudanar da zabe a Burma

Wani dan kasar Burma a lokacin da ya ke kada kuri'a
Image caption Ana gudanar da zabe a Burma

An bude rumfunan zabe a Burma don gudanar da babban zabe na farko cikin fiye da shekaru ashirin.

Tun da farko an yi ta haramta yakin neman zaben, inda masu sukar gwamnati ke cewa, sojoji sun ci gaba da rike madafun iko ta bayan fage, ta hanyar amfani da wasu da ke zame musu tamkar karnukan farauta.

Babbar kungiyar fafutikar tabbatar da dimokradiyya ta NLD, wacce Aung San Suu Kyi ke jagoranta ta kauracewa zaben.

Sai dai wani bangare na kungiyar ya shiga zaben, inda kuma a ka tsaurara matakan tsaro a Rangoon babban birnin kasar.

'Yan rajin kare mulkin dimokradiyya na gudanar da wata zanga-zanga a Sydney, babban birni Australia don nuna rashin gamsuwarsu ga yadda a ke gudanar da zaben.

Kasar Burma dai ta yi fice wajen ta ke hakkin bil adama.