Takaddama kan hukuncin sakin Tandja Mamadou

Shugaba Tandja
Image caption A watan Fabreru ne sojoji suka kifar da gwamnatin Tandja

A jamhuriyar Nijar an samu rarrabuwar kawuna a kan hukuncin kotun Kawancen Tattalin arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta yama ECOWAS ko CEDEAO ta yanke a yau.

Ko ta yi kira ne ga hukumomin majalisar mulkin sojan Nijar cewa su tsohon shugaban kasar, Tandja Mamadou, ba tare da wani sharadi ba.

Tun a watan biyu na bana ne sojin ke tsare da shi bayan da shuka hambarar da gwamnatinsa.

Yayin da wasu 'yan kasar, galibi magoya bayan Malam Mamadou Tandja suke marhabin da hukuncin kotun, wasu tsoffin yan adawa da Mulkin Toshon shugaban kasar kamar bangaren Jamiyyar PNDS TARAYYA, sun nuna takaicinsu da wannan matsayi na kotun.

Suna cewa kamata ma ya yi a gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin cin amanar kasa.

Take hakki

Yayin da take karanto hukunci da kotun ta yanke mai shari'a Awa Daboya Nana, ta ce ci gaba da tsare tsohon shugaban da gwamnatin mulkin sojan Nijar ke yi take masa hakki ne a mtsayinsa na bil'adama.

Wanda kuma ta kara da cewa hakan ya sabawa dukkan dokokin da aka tanada domin kare hakkin bil'adama a duniya.

Kotun ta kuma ce, takewa tsohon shugaba Tandja hakkinsa ya fito fili saboda gwamnatin sojan Nijar tana ci gaba da tsare shi tun daga ranar 18 ga watan Fabreru ba tare da an tuhume shi da wani takamaiman laifi ba, kuma ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba, har ya zuwa yanzu.

Kotun ta kuma kara da cewar, tsohon shugaba Tandja yana da hakkin a ba shi damar da ya nema ta ganin kwararrun likitoci da za su duba lafiyarsa a Tunisia ko kuma Morocco.

Tana mai cewa, kamata yayi gwamnatin mulkin sojan Nijar din ta yi la'akari da yanayin lafiyar tsohon shugaban.