Lauya ya kare kamfanin BP

 kamfanin BP
Image caption Malalar man kogin Mexico ta haifar da barna mai yawa

Lauyan da ke jagorantar binciken da Amurka keyi kan dalilan da suka haddasa matsalar malalar mai a tekun Mexico, ya ce har yanzu bai gano hujjar da ta nuna kamfanin BP na da laifi a malalar man ba.

Fred Bartlit, ya ce ya amince da kusan kashi casa'in na sakamakon binciken da kamfanin ya gudanar da ya dora akasarin laifin faruwar matsalar ga 'yan kwangila.

Sai dai lauyan da ke wakiltar mutanen da matsalar malalar man ta shafa Mike Stag, ya ce kamfanin na BP ya yi gaggawar komawa aiki ne saboda bukatarsa ta sake samun riba cikin gaggawa.

Matsalar malalar man wacce ita ce masifa mafi girma a tarihi da afkawa Amurka ta fuskar muhalli, ta jefa masunta da dama a yankin cikin damuwa da rashin tabbas.

Yayinda shi ma kamfanin na BP ya fuskanci babbar koma baya a harkokinsa.