'Yan sanda sun kama mutane 152 a Borno

Boko Haram
Image caption 'Yan Boko Haram sun yiwa 'yan sanda barna a Maiduguri

Rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke arewacin Najeriya, ta ce tana tsare da mutane 152 da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Kwamishin 'yan sandan jihar, Alhaji Mohammed Jinjiri Abubakar ne ya bayyana hakan a hirar da ya yi da BBC.

Ya ce mutanen sun hada da wadanda rundunar hadin gwiwa ta jami'an sojoji, da 'yan sanda, da jami'an tsaro na farin kaya wato SSS suka kama a lokacin wani sumame da suka kai unguwanni daban-daban a makonni ukun da suka gabata.

Ya ce: ''Mun samu labarin cewa akwai wuraren da suka boye makamai cikin Maiduguri, sun kai kamar bakwai. Cikin ikon Allah na je na zagaya su, ba komai a wurin.''

Sai dai mutane sun koka cewa, akasarin jami'an tsaron sun kame wadanda basu ji ba basu gani ba a lokacin sumamen.

Amma rundunar 'yan sandan ta ce tana gudanar da bincike domin tantance wadanda basu da laifi.