Shugaba Goodluck ya katse ziyarar zuwa Lagos

Shugaba Goodluck Jornathan
Image caption Shugaba Nigeria ya katse ziyararsa zuwa Lagos

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan, ya katse wata ziyara zuwa birnin Lagos a yau, domin jagorantar wani taron gaggawa da manyan kungoyoyin kwadago na kasar.

Wannan mataki dai wani yunkuri ne na kauce wa yajin aikin da kungiyar kwadagon ta lashi takwabin somawa daga ranar Laraba.

Ko a ranar Litinin dai an yi zama tsakanin bangaren gwamnatin da kuma kungoyoyin kwadagon ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Su dai kungoyoyin kwadagon, za su tsunduma cikin yajin aikin ne domin neman gwamnati ta biya su sabon tsarin albashi, wanda mafi karanci zai kasance Naira dubu goma sha takwas a wata.