Obama ya yabawa Indonesia

Shugaba Obama da Shugaba Susilo Bambang Yudhoyono
Image caption Shugaba Obama ya ce ana samun maslaha tsakanin kasashen musulmi da Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama ya yabawa Indonesia saboda yadda rikonta da mulkin dimokaradiya ya sauya rayuwar jama'a.

A ziyarar daya kai kasar, Mista Obama ya ce Indonesia , wadda ta fi kowace kasar musulmi girma da yawan jama'a a duniya, ta samu ci gaba ne sakamakon nasarar gwama ci gaban kasa da mutunta sauran addinai.

Ya gayawa taron jama'ar da ke jami'ar Indonesia ta kasar cewa, ya kamata su hada kansu duk kuwa da bambamce-bambancen da ke tsakaninsu.

Shugaban ya ce Amurka na samun galaba a yunkurin gyara lalatacciyar dangantakar da ke tsakaninta da kasashen musulmi.

Ya yi kira ga 'yan kasar su yi aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya.