Obama na ziyara a Indonesia

Obama na ziyara a Indonesia
Image caption Shugaba Obama yana karbar fareti daga sojojin Indonesia

Shugaban Amurka Barack Obama ya sauka a Jakarta babban birnin Indonesia, inda ake saran zai tattauna kan harkokin kasuwanci da kuma ci gaban siyasa.

Ana kuma saran zai yi amfani da ziyarar wajen ganawa da musulmin duniya, inda zai ziyarci masallaci mafi girma a kudu maso gabashin Asiya - masallacin Istiqlal.

Ziyarar Mista Obama zuwa kasar da tafi kowacce yawan musulmai a duniya, wani bangare ne na ziyarar kwanaki goma da shugaban ke yi a nahiyar Asiya.

Mista Obama na kuma ziyartar kasar da ya shafe shekaru hudu yana zaune lokacin da yake karami. Sai dai fadar White House ta ce shugaban zai takaita ziyarar tasa zuwa 'yan awanni kawai, saboda matsalar aman wutar da dutsen Marapi ke yi, wacce ka iya haifar da matsala ga tashi da saukar jirage.

Ana sa ran shugaban zai jinjinawa bunkasar tattalin arzikin kasar da kuma ci gaban da ta samu ta fuskar siyasa, a ganawar da zai yi da shugaba Susilo Bambang Yudhoyono.

Akwai yiwuwar shugabannin biyu za su sa hannu kan "cikakken shirin hadin guiwa" wanda suka amince da shi bara, wanda ya kunshi kasuwanci da tsaro da ilimi da zuba jari da kuma sauyin yanayi.