An kama wata mata da makamai a Maiduguri

Jami'an tsaro a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Jami'an 'yan sanda a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun kama wata mata dauke da makamai, wadanda suka hada da bindigogi kirar AK 47, da kuma albarusai.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bornon, Alhaji Muhammadu Jinjiri Abubakar, shine ya tabbatarwa BBC da labarin.

Ana zargin matar mai suna Lucy Dangana da yin safarar wadannan makamai daga kasar Chadi zuwa Najeriya.

A cewar matar, kayan ba nata ba ne, na wani dan uwanta ne da ya tsere.

Jihar Borno na daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro a Najeriya.

Jami'ai sun yi zargin ana shigo da makamai daga kasashen ketare zuwa jihar, inda wasu ke amfani da su wajen tada zaune tsaye.