Tattaunawa kan mulkin karba-karba

Shugaban jam'iyar PDP,Okwesilieze Nwodo
Image caption Ana tattaunawa kan tsarin mulkin karba-karba a Najeriya

A Najeriya, gwamnonin jihohi uku na arewacin kasar suna tattaunawa da na kudanci domin daidaita sabanin da ke neman raba 'ya'yan jam'iyyarsu ta PDP kan mulkin karba-karba a shugabancin kasar.

Su dai gwamnonin na jihohin Adamawa, da Sokoto da Jigawa sun gana ne a makon jiya, kuma nan da makon gobe ne suka ce za su sake yin wani taron dangane da wannan batu.

Gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako, ya shaidawa BBC cewa:''Zamu samu mu hada kai, mu yi abin da ya kamata.Batun na jam'iyyar PDP ne, kuma PDPn ba a arewa kadai take ba.Saboda haka 'yan kudu ma ya kamata mu kawo su cikin wannan magana''.

Tun bayan da shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar ne dai a ke ci gaba da cece-kuce dangane da batun na karba-karba a kasar.