Shugaba Sarkozy ya sa hannu kan dokar fansho

Dokar fansho
Image caption Ayar dokar ta haifar da zanga-zanga a kasar

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya saka hannu kan dokar sauya tsarin fansho wadda kungiyoyin kwadago na kasar suke matukar adawa da ita.

An dauki kimanin watanni biyu ana gudanar da zanga-zanga wacce ta kawo rikici a kasar ciki har da datse matatun mai da gidajen dibar man.

Dokar ta daga shekarun yin ritaya daga aiki daga shekara sittin zuwa shekara sittin da biyu.

Sabanin shugabannin kasar da suka gabace shi, Shugaba Sarkozy ya tsaya kai da fata, ya ki ba da kai bori ya hau duk da tsattsaurar adawar da shirin nasa ya fuskanta a kan titunan kasar.

Sa hannun Nicolasa Sarkozy a kan wannan doka dai na je-ka-na-yi-ka ne, musamman ma kasancewar majalisar dokokin kasar ta gaggauta amincewa da ita don yayyafa ruwa a kan wutar zanga-zangar da ma'aikata suka yi ta yi.

Gaggawa

Ranara Talata ne dai kotun tsarin mulki ta yi watsi da bukatar da 'yan adawa masu ra'ayin gurguzu suka shigar a wani yunkuri na karshe don hana kudurin dokar kaiwa gaci.

Kusan nan take dokar ta fito a mujallar hukuma wadda ake wallafa sabbin dokoki a cikinta, abin da ke nuna cewa shugaban kasar ya rattaba mata hannu ne 'yan mintunan kadan bayan kotun ta yanke hukuncin.

Kungiyoyin kwadago dai na ci gaba da nuna adawa, har ma sun yi kiran a sake yin zanga-zanaga ranar 23 ga watan Nuwamba.

To amma babu ko tantama amincewa da wannan doka wani muhimmin al'amari ne ga wannan gwamnatin, don kuwa shi ne kashin bayan sauye-sauyen da Mista Sarkozy ke aniyar aiwatarwa.