Zanga-zangar 'yan kwadago a Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Shugaba Jonathan ya kasa shawo kan kungiyar kwadagon

Hadaddiyar kungiyar kwadago da masu fafutukar kare hakkin bil'adama sun gudanar da zanga-zangar goyon baya ga yajin aikin da suka fara a ranar Laraba.

Zanga-zangar wacce aka gudanar a babban birnin kasuwancin kasar na Legas, an shirya ta ne domin tallata bukatun ma'aikatan Najeriyar, wadanda suka fara yajin aiki na gargadi na tsawon kwanaki uku.

Kungiyoyin sun karade hanyoyin jihar Legas inda suke ta shelar 'yan Najeriya su fito dan yaki da manufofin gwamnatin da suka kira marasa alfanu ga talakawa.

Makarantu da bankuna da ofisoshin gwamnati sun kasance a rufe, yayinda a Legas, motocin haya na gwamnati da dama ba su fito aiki ba.

Tattaunawar da aka yi tsakanin shugaban Najeriya, Dakta Goodluck Jonathan da shugabannin kwadagon a daren jiya ta tashi baram- baram.

'Yan kungiyar kwadagon na bukatar gwamnatin tarayyar Najeriyar ce ta biya naira dubu goma sha takwas a matsayin albashi mafi karanci ga ma'aikata.

Sai dai duk da wannan yajin aiki, shugabannin kwadagon za su yi wani taro don sake duba matsayinsu game da yajin-aikin.