Cameron ya yi Allah wadai da tashin hankali

Dalibai na zanga-zanga
Image caption Dalibai sun kutsa kai hedkwatar jam'iyyar Conservative

Pira ministan Burtaniya David Cameron ya yi Allah wadai da tashin hankalin da ya biyo bayan zanga-zangar da dalibai suka gudanar bisa karin kudin makaranta.

Pira ministan ya ce tashin hankalin na tsakiyar London, da ya janyo aka kama mutane 35 sannan 14 suka samu rauni, ba za a "amince da shi ba".

Ya yabawa kokarin da 'yan sanda suka yi na shawo kan matsalar, amma ya ce "basu da yawa". Shugaban 'yan sandan birnin London Sir Paul Stephenson, ya bayyana hargitsin na ranar Laraba da cewa "abin kunya ne".

'Yan sanda uku ne suka samu raunuka a lokacin hargitsin wanda ya faru a wajen hedkwatar jam'iyyar Conservative mai mulki a Westminster .

Wasu masu zanga-zangar sun kutsa kai cikin ginin, sai dai daruruwan ma'aikatan jam'iyyar an riga andebe su.

Mista Cameron ya ce ya kalli abin da ya faru a birnin Seoul na Koriya ta Kudu inda yake halartar taron kasashen G20.

"Na damu sosai da lafiyar jama'ar da ke cikin ginin, nasan jama'ar da suke aiki a ginin ba wai kawai 'yan jam'iyyar Conservative ba, don haka na yi magana da su ta wayar tarho," in ji cameron.

Sai dai Mista Cameron ya ce ba zai sauya matsayinsa kan karin kudin makarantar ba - wanda zai baiwa makarantu damar karbar fan dubu 9 daga dalibai a matsayin kudin makarantar shekara guda.