Jam'iyyar CPC ta nemi Jonah Jang yayi murabus

Gwamnan jahar Filaton Najeriya Jonah Jang
Image caption Jam'iyyar CPC reshen jahar Filato ta nemi gwamnan jahar daya gaggauta yin murabus daga mukaminsa na gwamna

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta CPC a jihar Filato ta bukaci gwamnan jihar, Jonah Jang, da ya gaggauta yin murabus daga kan kujerarsa.

Jam'iyyar ta CPC dai ta ce, gwamnan ya kasa samar da zaman lafiya a jihar ta Filato, tace kuma ya gaza cika alkawuran da ya yiwa jama'ar jihar a lokacin da ya kama aiki.

Jam'iyyar ta CPC ta kara da cewar an sami asarar rayuka a jahar a zamaninsa don haka wannan ya nuna cewar gwamnan ba zai iya shugabancin jahar ba.

To sai dai kuma mai magana da yawun gwamnan Jahar Filaton yace zancen gwamnan yayi murabus abin dariya ne, domin a cewarsa ba jihar Filato ce kawai ake samun tashe-tashen hankulla ba a Najeriya.