'Intanet na fuskantar barazana'

Intanet

Da alama fasahar intanet za ta fuskanci rashin tabbas na tsawon shekaru a daidai lokacin da take kokarin komawa sabon tsarin adireshinta.

Daya daga cikin mutanen da ake kira iyayen intanet Vint Cerf ne ya yi wannan gargadin a daidai lokacin da kasar Burtaniya ke yunkurin komawa sabon adireshin.

Ana sa ran naui'in adireshin intanet da ake da shi a yanzu zai kare a cikin shekarar 2012, a don haka ya kamata kasashe da kamfanoni su fara komawa sabon adireshi, in ji Mr Cerf.

Jami'in ya kuma kara da cewa, a lokacin sauyin adireshin, rariyar likau da dama za su kasance da rashin tabbas, hakan kuma zai sa a fuskanci matsaloli wajen ziyartar wasu shafukan na intanet.

Fasahar intanet dai ta kai matsayin da take a kai ne a yau ta hanyar amfani da samfuri na hudu na tsarin adireshinta wato (IPv4), wadda ke bada damar a yi rajistar adireshin intanet biliyan 4.3.

Kididdiga ta nuna cewa wannan adadin na adireshi zai kare a karshen watan Janairun shekarar 2012.

Batutuwa masu muhimmanci

An kirkiro da wani tsarin da zai samar da karin adireshi mai yawa fiye da wanda ake da shi a yanzu wanda aka sanya wa suna IPv6, sai dai ana samun tafiyar hawainiya wajen amfani da shi.

Mr Cerf ya soki kamfanoni da cewa, ba su da hangen nesa, shi ya sa suke jan kafa wajen fara amfani da tsarin wanda zai taimaka musu wajen bunkasa harkokinsu.

Ya ce za a samumatsala wajen komawa sabon tsarin, saboda tsare-tsaren guda biyu ba za su iya aiki tare da juna ba.

Yayinda wani bangare na fasahar ta intanet ya koma amfani da tsarin IPv6, wadanda suke son ziyartar wasu shafuka dake amfani da tsarin IPv4 ba za su samu damar yin hakan ba.

Fasahar ta intanet ba za ta daina aiki ba a lokacin yin sauyin, sai dai samun wasu shafukan na intanet zai gagara.

Kuma wannan rashin tabbas din zai dauki shekaru in ji Mr Cerf, saboda kamfanin matambayi-ba-ya-bata na Google, sai da ya dauki shekaru kafin ya iya tayar da sabon tsarinsa na IPv6.

Tafiyar hawainiya

Mr Cerf ya ce a yanzu kashi daya cikin dari na bayanan da ake tura wa ta hanyar fasahar ta intanet ce ke bi ta sabon tsarin adireshin IPv6, a don haka ya kamata kasashen duniya su bayar da fifiko ga kokarin komawa sabon tsarin.

Kasashe irinsu China da Jamhuriyar sun yi hobbasa wajen amfani da sabon tsarin na IPv6, yayinda wasu kasashen ko farawa ma ba su yi ba.

Shi ma Nigel Titeley, shugaban kamfanin da yake bayar da adireshin intanet a karkashin tsarin IPv4 a Turai ya ce, nan gaba kadan matsalar karancin adireshin intanet za ta fara shafar kamfanoni.

Ya ce kokarin janyo hankalin karin mutane su yi amfani da fasahar ta intanet da kuma bunkasa harkokin kasuwanci a intanet ka iya fuskantar koma baya saboda rashin adireshi.