An kafa sabuwar gwamnati a Iraki

Tutar Iraqi
Image caption Ko sabuwar gwamnatin za ta iya kawo zaman lafiya?

Majalisar dokokin Iraq ta zabi sabon kakaki a wani muhimmin bangare na yarjejeniyar raba madafun iko da aka cimma tsakanin manyan jam'iyyun kasar, watanni takwas bayan zaben da babu wani bangare da ya samu cikakkiyar nasara.

akakin da majalisar ta zaba dai shi ne Osama al-Nujaifi, na kawancen Iraqiyya wadanda mafi yawansu yan Sunni ne.

Ana kuma sa ran majalisar za ta sake zabar shugaban kasa Jalal Talabani, wani Bakurde, shi ne inda shi kuma zai gaiyaci firaminisata mai ci a yanzu Nouri al-Maliki, wanda dan Shi'a ne da ya kafa sabuwar gwamnati.

Karatun kenan daga al-Qur'ani mai tsarki da aka bude zaman majalisar dokokin Iraqin da shi a yammacin yau.