Gwamnatin Nijar za ta kalubalanci neman sakin Tanja

Tandja Mamdou
Image caption Gwamnatin Nijar ba za ta gurfanar da Tandja Mamadou gaban kotu ba

Hukumomin Nijar sun nuna cewa ba su amince da hukuncin da kotun kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO ta yanke, cewa ta su saki tsohon shugaban kasar, Tandja Mammadu, wanda gwamnatin mulkin sojin kasar ke tsare da shi tun bayan da ta hambarar da shi a farkon bana.

Kakakin gwamnatin ta Nijar, Muhamman Lawalli Dan Da, shi ne ya bayyana haka a hira da BBC.

Ya ce suna tunanin daukar wasu matakai na shari’a. Yana cewa dalilan tsaro ba za su ba da damar sakin tsohon shugaban ba a halin yanzu.

Ya kuma nuna alamar ba su da wata niyya ta gurfanar da shi a gaban kotu a halin yanzu.