Obama ya ja kunnen Koriya ta Arewa

Taswirar Koriya ta Arewa
Image caption Shugaba Obama ya nemi Koriya ta Arewa data dakatar da shirinta na nukiliya

Shugaba Obama na Amurka ya ja kunnen Koriya ta Arewa, akan ta dakatar da shirinta na nukiliya, ko kuma a maida ita saniyar ware a duniya.

Shugaba Obama wanda yanzu haka yake ziyara a Koriya ta kudu, ya kuma halarci wani bukin tuna mazan jiya da aka yi, domin tunawa da yakin Koriya da aka yi a shekarun alif dari tara hamsin.

Obama ya kuma ce, Amurka za ta ci gaba da baiwa Koriya ta Kudu tallafi ta fuskar tsaro, ya kuma ce, kawance na kara karfi tsakanin Amurkar da Koriya ta kudu.

Shugaban na Amurka ya kuma kara da cewa, shirin nukiliyar Koriya ta Arewa, yana kan hanyar zama wata takalar fada.