Tarihin Didier Drogba

Didier Drogba
Image caption Didier Drogba ba kanwar lasa ba ne a fagen kwallo

A ranar farko ta kakar 2009/2010, Hull City na gaban Chelsea, har sai da Drogba ya ci kwallaye biyu sannan ya ceto su. Kuma wannan ne mafari.

Tun watan Janairun 2010, Drogba ya ci gaba da ruwan kwallaye a kungiyar sa da kuma kasa baki daya.

Ya zira kwallaye 37 a wasanni 40 da ya buga wa Chelsea, inda ya taimaka wa Chelsea ta lashe kofunan Premier da na FA, sannan ya zamo dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a gasar Premier.

Shi ne kawai ya nuna kansa a tawagar Ivory Coast a gasar cin kofin kasashen Afrika da kuma ta duniya a 2010.

Sai dai an ambato shi yana cewa bai damu da cin kwallaye ba, illa dai kawai ya taimaka a yi nasara, abinda yasa yake taimakawa irinsu Kalou da Malouda da Anelka.

Drogba na daya daga cikin ‘yan wasa mafiya kwarewa a fagen tamola a yau. Duk da cewa sha’awarsa da kwallo kan sa shi ya yi ba daidai ba a wasu lokutan.

Ra'ayin kwararru - da Oluwashina Okeleji

Ni dai zan zabi Didier Drogba, saboda yadda yake zira kwallaye akai-akai- masu amfani ga duka kungiyarsa da kuma kasarsa.

Kuma ya bayyana cewa bai damu da ya zira kwallo ba, illa dai kawai ya taimakawa abokan wasansa su samu nasara.

Za ka iya tambayar Nicolas Anelka da Solomon Kalou da Florent Malouda, me yasa cin kwallo ke zuwar musu cikin sauki idan suna buga wasa tare da Drogba.

Babu wani dan wasa daga Afrika da ya fara kakar bara cikin nasara kuma sannan ya kare cikin nasara kamar Drogba.

Ya zira kwallaye 37 a wasanni 40 da ya bugawa Chelsea, inda ya taimakawa Chelsea ta lashe kofunan Premier da na FA, sannan ya zamo dan wasan da ya fi kowa zira kwallaye a gasar Premier.

Shi ne kawai ya nuna kansa a tawagar Ivory Coast a gasar cin kofin kasashen Afrika a Angola.

Amma bayan ya dawo daga Angola, sai ya nuna cewa rashin nasarar ta kasar ce kawai – inda ya ci gaba da ruwan kwallaye a Chelsea.

Rashin lafiya ta sanya shakku kan yiwuwar taka rawarsa a gasar cin kofin duniya. Amma daga baya ya warke kuma ya jagoranci kasar a wasanni ukun da suka buga.

Duk da cewa Ivory Coast na rukuni mai tsauri, amma Drogba ya zira kwallo daya a wasan da Brazil ta doke su da ci 3-1.

Kusan kowa zai amince cewa idan yana kan ganiyarsa to za a sha ruwan kwallo, kuma ba kowanne dan wasa ne ke da karfi da kuzarin da Drogba ke da shi ba.

Sai dai yakan yi fushi wani lokacin – abinda kuma ba ya taimaka masa.

Sai duk karfi da kuzarin da yake da shi, yana yawan faduwa kamar wanda aka harba da bingida.

Ko ta yaya ka kalli wannan lamari, akwai banbanci tasakanin Drogba da sauran ‘yan wasan da ke taka leda a irin matsayinsa. Zai yi wuya mutum ya kasa zabar Didier Drogba a matsayin zakaran kwallon Afrika na BBC a karo na biyu a jere.

Za ku iya zaban ne ta hanyar latsa wannan rariyar likau din da ke biye:

http://www.bbc.co.uk/worldservice/africa/2010/11/101111_afoy_2010_vote_page.shtml

Ko kuma ta lambar waya +44 7786200070