Tarihin Samuel Eto'o

Samuel Eto'o
Image caption Samuel Eto'o yana taka rawa sosai a Inter Milan

A shekara ta 2010, Samuel Eto’o ya kara karfafa matsayinsa a fagen kwallon kafa a duniya, lokacin da ya lashe gasar cin kofin zakarun Turai a karo na uku.

Bayan nasarar da ya samu da Barcelona a shekarun 2006 da 2009, nasarar da ya samu da Inter Milan a Italiya, ta nuna cewa ya lashe kofin sau biyu a jere da kungiyoyi daban-daban.

Adadin kofunan da dan wasan ya dauka sun karu, bayanda ya lashe gasar zakarun Turai da Serie A da kuma Coppa Italia, shekara guda bayan ya lashe irinsu da Barcelona – Dan wasan na Kamaru ya zamo dan wasa na farko a tarihi da yayi hakan.

Shi ne ya zira kwallo mai mahimmanci ga Inter Milan wacce ta kaisu ga fitar da Chelsea a gasar zakarun Turai a watan Maris.

Bayan da Rafa Benitez ya canji Jose Mourinho a Inter, Eto’o ya yi amfani da damar sauya yanayin wasan da sabon kociyan ya yi, da kuma raunin da Militto ya samu, inda ya kara nuna bajintarsa.

Shi ne dan wasan da ya fi kowa zira kwallo a gasar zakarun Turai ta bana, inda ya zira kwallaye bakwai a wasanni hudu kacal. Yayinda ya ci kwallo bakwai a wasanni tara a gasar Serie A, wacce ake ganin tafi kowacce kwararrun ‘yan baya.

A wasan kasa da kasa, dan wasan ya samu koma baya a wannan shekarar.

Tawagar Indomitable Lions bata taka rawar gani a gasar cin kofin kasashen Afrika da kuma ta duniya ba – amma duk da haka Eto’o ya yi kokari inda ya zira kwallaye hudu a wasanni bakwai da ya buga a Angola da kuma Afrika ta Kudu, duk da cewa shi kadai aka sa a sama.

Amma duk da haka kokarin da ya yi a kungiyarsa ya sa hukumar FIFA ta sanya shi a jerin ‘yan wasan da za a zabi zakaran dan kwallon duniya daga cikinsu.

Ra'ayin kwararru - da Piers Edwards

Ya kamata Samuel Eto’o ya zamo zakaran kwallon Afrika na BBC, saboda akwai ‘yan wasa da dama ba wai daga Afrika ba, har ma a duniya baki daya, wadanda ba su yi abinda ya yi ba.

A watan Mayu ya zamo dan wasa daya tilo da yaci kofuna uku sau biyu-biyu a jere, ya lashe gasar zakarun Turai da Serie A, da kuma Coppa Italia, shekara guda bayan ya lashe irinsu da Barcelona.

Ya taka rawa sosai ganin cewa an sa shi a lambar da bai saba bugawa ba, kuma nauyin da ke kansa yana da yawa.

A karkashin jagorancin Benitez, dan wasan na Kamaru ya nuna kwarewarsa inda ya zira kwallaye 14 a loakacin da ake rubuta wannan sharhi, a wasanni 13 da ya buga a Serie A da kuma gasar zakarun Turai.

Rashin nasarar Kamaru ita ce kawai take tasayawa tsakanin Eto’o da wannan kyauta – amma shi za a zarga kan rashin nasarar da for Le Guen a Angola da kuma Afrika ta Kudu.

Za ku iya zaban ne ta hanyar latsa wannan rariyar likau din da ke biye:

http://www.bbc.co.uk/worldservice/africa/2010/11/101111_afoy_2010_vote_page.shtml

Ko kuma ta lambar waya +44 7786200070