Shugaba Obama yayi kira ga sabuwar gwamnatin Iraqi

Shugaban Amurka Barack Obama
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci sabuwar gwamnatin kasar Iraqi data samu wakilcin kowanne bangare na al'ummar kasar

Shugaba Barack Obama na Amurka yayi kira ga shugabannin kasar Iraqi su kafa gwamnati wadda zata samu wakilcin kowanne bangare na al'ummar kasar, bayan zaman majalisar dokokin Iraqin da ya kusa jefa kokarin kafa gwamnatin cikin rudani.

Wata sanarwa daga fada White House tace, shugaba Obama ya jaddada bukatar ganin cewa, shugabannin dukkan bangarorin al'ummar Iraqi sun samu wakilci a sabuwar gwamnatin da za'a kafa

Rantsar da Jalal Talabani a matsayin shugaban kasa, da kuma Nuri Al Maliki a matsayin Firayim Minista, shi ne matakin farko na kafa sabuwar gwamnati a Iraqi.

Mambobin mabiyya sunni dai sun fice daga bikin rantsar da sabuwar gwamnatin tunda farko bayan da sukai zargin cewar babu wakilcin mambobin jam'iyyar Marigayi saddam Hussein ta Baath