Manouchehr Mottaki na Iran ya gana da takwaransa na Najeriya

Shugaban Ahmadenajad na Iran
Image caption Ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da takwaransa na Najeriya makonni biyu bayan wasu kwantenoni da aka kama dauke da makamai da suka fito daga kasar ta Iran

Ministan hulda da kasashen waje na Iran, Manouchehr Mottaki ya gana da takwaransa na Najeriya, makonni biyu bayan an gano wasu makamai da aka ce sun fito ne daga Iran zuwa Najeriya.

Shi dai Manouchehr Mottaki ya gana ne da takwaransa na Najeriya, Odein Ajumogobia a Lagos inda nan ne jami'an tsaro suka kama makaman.

Kamfanin zirga-zirgar jiragen ruwa na Faransa, wato CMA ne dai yace, makaman dake cikin kwantenonin da aka kama, an loda su ne a tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas dake Iran.